Muna zargin ‘yan sandan Kano sun hada kai da gwamnati domin cutar da mu – NNPP

0
94

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta zargi kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda da hada kai da gwamnatin jihar ta APC domin kawo mata nakasu a zabe mai zuwa.

A wani taron manema labarai da ta kira, Jam’iyyar ta NNPP ta ce kwamishinan ‘yan sandan ya kame mambobinta sama da 100 ba tare da wani dalili ba, inda ta yi kira ga babban sufeton ‘yan sandan kasar ya cire kwamishinan jihar.

Dr Abdullahi Baffa Bichi, wanda shi ne dan takarar Sanata na jam’iyyar, ya shaida wa manema labaran cewar sun bada tsawo sa’o’i 24 a saki mambobinsu ko su tsunduma zanga-zangar lumana.

Wakilin RFI Hausa, Abubakar Abdulkadir Dangambo ya yi kokarin jin ta bakin ‘yan sandan na Kano kan wannan zargi, sai dai har zuwa yanzu kakakin rundunar bai amsa kiran da manema labarai suka yi masa ba.

Kazalika, ita ma gwamnatin Kano ba ta ce komai tukunna game da zargin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here