Mutum 17 sun tsira daga hatsarin jirgin ruwa a Legas

0
104
 

Akalla fasinjoji 17 aka kubutar a ranar Litinin bayan da wani jirgin ruwa ya kife daura da gadar ‘Third Mainland Bridge’ da ke Jihar Legas.

Jirgin na ‘yan kasuwa mallakar kamfanin Fazma ya kife ne, bayan ya taso daga tashar Ikorodu da misalin karfe 6:45 na safiyar ranar kafin ya isa zuwa yankin Ebute Ero.

A cikin sanarwar da Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar, ta fitar ta bayyana cewa, jirgin ruwan ya kife ne da misalin karfe 7 na safiyar Litinin.

A cewar hukumar ta LASWA, an samu nasarar kubutar da daukacin fasinjojin tare da ma’aikatan jirgin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here