Karamin ministan albarkatun man fetur, Cif Timipre Sylva, ya ce nan ba da dadewa ba Najeriya za ta samu ganga miliyan biyu na danyen mai a kullum.
Ministan, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Horatius Egua, ya fitar, ya danganta asarar kudaden shigar da ake samu daga hako danyen mai da sata, fasa bututun mai da gurbatacciyar ababen more rayuwa, amma ya lura cewa gwamnati na magance hakan.
Ya ce, “Muna da kwarin gwiwa cewa Nijeriya za ta cimma burin hako danyen mai ganga miliyan biyu a kowace rana nan ba da jimawa ba. Gwamnati na yin duk mai yiwuwa don isa inda ya kamata kuma kowa yana aiki tukuru don cimma hakan.
Shugaban rukunin kamfanin na NNPC, Mele Kyari, a ranar juma’a, ya ce yawan danyen mai ya karu zuwa ganga miliyan 1.6 a kowace rana daga kusan ganga 1m a karshen shekarar da ta gabata bayan farmakin da aka kai wa barayin mai.
Shugaban rukunin kamfanin na NNPC, Mele Kyari, a ranar Juma’a, ya ce yawan danyen mai ya karu zuwa ganga miliyan 1.6 a kowace rana daga kusan ganga 1m a karshen shekarar da ta gabata bayan farmakin da aka kai wa barayin mai.
Don haka ya bukaci Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) da Hukumar Kula da Man Fetur ta Midstream da Downstream (NMDPRA) da su yi aiki tare don tabbatar da cewa an magance matsalolin da kalubalen da ke gabatowa a cikin ingantacciyar yawan samar da danyen mai don bunkasa kasa da kudaden shiga.