Karancin kudi: Za a iya sayen kuri’a da abinci — El-Rufai

0
98

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce akwai sauran hanyoyin da ‘yan siyasa za su iya bi don siyan kuri’a ba tare da kudi ba.

El-Rufai ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Litinin.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake tunanin ‘yan siyasa sun tara kudade gabanin zabukan 2023, don amfani da su wajen siyan kuri’ar masu zabe.

Ya dage cewa gwamnonin jam’iyyar APC suna adawa da manufar sauya fasalin Naira, saboda wahalar da ta jefa mutane a ciki ba wai don sayen kuri’a ba.

“Yau aka fara siyan kuri’a? Me yasa tun a baya ba a sauya fasalin kudin ba? Me ya sa sai yanzu? Na biyu, ana sayen kuri’a ne kawai da kudi? Ana iya siyan ta da da Dala, Yuro, Sefa, za kuma a iya bai wa masu jefa kuri’a abinci.

“Ba za a iya cire kudi daga siyasa ba, amma za a iya rage yaduwarsu.

“Ba ma adawa da wannan manufar saboda sayen kuri’a. Na rantse da Allah muna adawa da shi ne saboda yadda mutane ke shan wahala, ba saboda zabe ba,” in ji El-Rufai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here