‘Yan siyasa na rike da sama da Naira bilyan dari biyar na tsofaffin kuɗi don siyan kuri’u – EFCC

0
105

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Abdulrasheed Bawa, ya ce ‘yan siyasa na rike da sama da Naira bilyan 500 na tsofaffin kuɗi wanda ba a kai ga mayar wa Babban Bankin Ƙasar ba.

Abdulrasheed Bawa ya bayyana hakan ne a wani shiri na gidan talabijin na Channels na siyasar mu a yau.

Ya ce hukumar ta samu bayanai da ke nuna cewa ‘yan siyasa na shirin amfani da wasu hanyoyi na sayan kuri’a lokacin zaɓe.

‘Yan siyasa basu da wata mafita a yanzu illa ta sayan kuri’u saboda sun ga na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS za ta kawo musu cikas. Wannan bayanan sirri ne da muka samu. Sai dai, ina farin cikin cewa dukkan hukumomin tsaro na aiki tukuru wajen ganin an gudanar da zaɓen lami lafiya,” in ji Bawa.

Shugaban na EFCC ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su bai wa kungiyar haɗin-kai a ƙoƙarinta na yaki da masu sayan kuri’a a zaɓen Shugaban ƙasa da na ‘yan Majalisar Tarayya da za a gudanar ranar Asabar.

Ya kuma buƙaci ‘yan ƙasar da su zaɓi mutane masu dattako da sanin ya kamata a zaɓen da ke tafe.

A cewarsa, sayan kuri’a babban batu ne da ke shafar makomar Najeriya da kuma ‘yan ƙasar, don haka ya kamata a dakatar da hakan ta kowace hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here