‘Yan takarar shugaban kasa sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

0
104

Masu neman kujerar shugabancin kasa a Najeriya, sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja, gabanin zaben kasar da zai gudana ranar Asabar mai zuwa.

Daga cikin wadanda suka halarci taron zaman lafiyar, akwai Omoyele Sowore na jam’iyyar AAC, Bola Tinubu daga APC da kuma Peter Obi na jam’iyyar LP.

Sauran sun hada da Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP, da kuma Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari tare da tsohon shugaban Kenya Jomo Kenyata  da kuma tsohon shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki na daga cikin wadanda suka halarci taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here