APC ta bukaci a gudanar da bincike kan rikicin siyasa da ya barke a Kano

0
94

Kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar APC, ya bukaci ‘yan sanda da su binciki fadan bangar siyasa da barnar da aka yi a Karamar Hukumar Kumbosto a ranar Alhamis.

Mataimakin kakakin kwamitin, Alhaji Garba Yusuf ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai ranar Alhamis a Kano.

Kwamitin ya yi watsi da zargin cewa akwai hannun magoya bayan jam’iyyar APC a rikicin, inda ya ce ya kamata ‘yan sanda su binciki lamarin tare da gurfanar da masu hannu a tashin-tashinar.

“Duk wadanda ke da hannu aa harin da aka kai wa mazauna yankin za a gurfanar da su gaban kotu.

“APC ba ta da hannu ta kowacce hanya kuma ba mu san abin da ya faru ba.

“A madadin kwamitin yakin neman zabe, mun yi Allah wadai da wannan aika-aika, kuma za mu rubuta wa ‘yan sanda da su gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da gurfanar da duk wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya,” in ji shi.

A ranar Alhamis dai Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC), ta tabbatar da cafke mutum 55 da ake zargi biyo bayan harin da wasu ‘yan daba suka kai kan wasu mutane tare da lalata motoci a kan hanyar Zariya.

Ana zargin magoya bayan APC da na NNPP sun yi arangama da juna, lamarin da ya yi sanadin jikkatar wasu tare da salwantar dukiyoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here