Buhari da iyalan sa sun isa Katsina don yin zabe

0
98

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa mahaifarsa Daura da ke Jihar Katsina don ci gaba da shirye-shiryen zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da za a yi a ranar Asabar.

Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari da darakta-janar na hukumar tsaron NIA, Ahmed Rufai Abubakar ne suka tarbe shi.

Buhari zai kada kuri’arsa ne, tare da mai dakinsa Aisha Buhari da kuma sauran iyalansa a Daura.

A cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu, ya fitar ya ce, jirgi mai saukar angulu da ya dauko Buhari, ya isa a Daura.

Sanarwar ta kara da cewa, ganin irin mahimmancin da kowace kuri’a daya ke da shi, Buhari ya sa a yi wa iyalansa, ciki har da tawagarsa rijista don su kada kuri’insu a Daura.

Kafin Buhari ya tashi zuwa Daura, ya halarci gangamin yakin neman Bola Ahmed Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here