Gobara ta kashe ma’aurata da ’ya’yan su 6 a Zariya

0
119

Mutum takwas ’yan gida daya sun rasu a wata gobara a tsakiyar dare a Unguwar Tankin Toliya, Hayin Ojo a Karamar Hukumar Sabon Garin Jihar Kaduna.

Gobarar da ta tashi da misalin karfe 2 na dare ta yi ajalin wani maigidancin nai suna Malam Rabi’u da matarsa mai jego da jaririnsu dan kasa da kwana 40 da sauran ’yayansu biyar.

Wani makwabcinsu mai suna Malam Janaidu Muhammad ya ce jama’a sun yi kokarin kashe ceto ’yan gidan saboda rashin zuwan jami’an kwana-kwana, amma babu abin da aka iya fitarwa daga ciki.

Sai dai ya ce kafin a kai ga dakin da mutanen gidan suke ciki domin ceto su, duk sun riga sun kone, in bada yaro daya da aka ceto shi da ransa, shi ma ko da aka kai shi asibiti, ya ce ga garinku nan.

Gobarar babu wadda zai iya bayyana sanadinta, kuma kokarinmu wakilinmu na jin ta bakin jami’a kashe gobara da ke shiyyar bai yi nasara ba.

Wakilinmu  ya je ofishinsa amma bai same shi ba, wadanda aka tarar a ofishin kumka suka ce sun ce ba za su ce komai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here