A ranar Alhamis ne wata kotun majistare da ke birnin Jos ta yanke wa wani ma’aikaci mai shekaru 35 mai suna Fwangmun Danung hukuncin daurin shekara guda a gidan yari bisa samunsa da laifin zagi da kuma tsoratar da mahaifinsa.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa alkalin kotun, Mista Tapmwa Gotep, ya yankewa Danung hukuncin bayan ya amsa laifinsa .
Gotep ya ba shi zabin tarar Naira 10,000 ko wata shida bisa laifin zagin mahaifinnasa da kuma wata shida ba tare da biyan tarar mahaifinsa ba.
Alkalin ya ce hukuncin zai zama katabus ga masu son aikata irin wadannan ayyuka.
Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Insifekta Frank Alex, ya shaida wa kotun cewa an kai karar ne a ranar 26 ga watan Disamba, 2022, a ofishin ‘yan sanda na Rantya ta hannun mai shigar da kara, Othniel Danung.
An ce wanda aka yanke wa hukuncin ya finciko mahaifinnasa daga cikin gida kuma ya yi masa zagin tsamar nama.
Mai gabatar da kara ya ce wanda ake tuhumar ya kunna iskar gas kuma ya yi barazanar kona gidan da mahaifinnasa ya ke ciki.
Mai laifin ya kuma bukaci mahaifinsa da ya biya shi bashin da yake binsa na N200,000.
Laifin yaci sabawa sashe na 377 da 379 na dokar Penal Code ta Jihar Filato.