Sharhin da wasu jaridu suka yi game da zaben shugaban kasa

4
257

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito tsohon shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Attahiru Jega na bayyana gamsuwarsa da irin shirin da Hukumar INEC ta yi domin gudanar da wannan zabe na yau.

Jega ya ce tun daga shekarar 2007 zaben Najeriya na ci gaba da samun inganci, yayin da wannan sabuwar na’urar BVAS da za’a yi amfani da ita a karo na farko a wannan shekara, za ta zama zakarar gwajin dafi wajen kara ingancin zaben.

JARIDAR PREMIUM TIMES ta mayar da hankali ne akan dubban ‘yan Najeriyar da yau ba za su damar kada kuri’a ba, saboda matsalar tsaron da ta addabi yankunan su.

Jaridar ta bayyana irin wadannan yankuna da matsalar ta fi kamari da suka hada da arewa maso gabashin Najeriya, mai fama da rikicin boko haram, da arewa maso yamma, mai fama da rikicin ‘yan bindiga, da kuma kudu maso gabas mai fama da rikicin kungiyar IPOB da ke fafutukar kafa kasar Biafra.

JARIDAR FINANCIAL TIMES ta bayyana zaben Najeriya na yau a matsayin wani tsere na mutane 3, tsakanin Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar da Peter Obi.

Jaridar ta ce fitowar Peter Obi ya sauya yadda manyan jam’iyyu 2 ke mamaye shirin zaben kasar.

JARIDAR LIBERATION ta Faransa ta ruwaito cewar fafutukar ‘yan ta’adda da kabilanci da gaba da rikici tsakanin manoma da makiyaya da kuma aikata wasu manyan laifuffuka ne za su mamaye shirin zaben Najeriya da za’a gudanar yau asabar.

Jaridar ta ce wasu daga cikin wadannan matsaloli na iya yiwa zaben barazana.

JARIDAR DAILY GRAPHIC ta kasar Ghana ta ce yau asabar za a gudanar da zabe mafi girma a nahiyar Afirka, inda masu kada kuri’a sama da miliyan 93 za su zabi shugaban kasa a Najeriya, a karawa mafi girma da za a gani.

Jaridar ta ce bayan zaben shugaban kasa, akwai kuma kujerun majalisar dattawa 109 da na majalisar wakilai 360 da za’a fafata.

JARIDAR NATION ta kasar Kenya ta bayyana wannan zabe a matsayin karawar jam’iyyu 2 tsakanin PDP da APC, yayin da ta kara da cewar zaben na da matukar muhimmanci ga Kenya da duniya baki daya,  saboda tasirinsa da kuma yadda dangantaka za ta dore tsakanin kasashen biyu bayan rantsar da sabon shugaban kasa.

JARIDAR TIMES ta kasar Afirka ta kudu ta mayar da hankali ne akan yadda wannan zaben na Najeriya ya dauke hankalin matasan dake neman chanji, duk da yake cikin manyan ‘yan takarar babu mai kasa da shekaru 50.

4 COMMENTS

  1. Gaskia wannan xabeh masha Allah ammah muh indah mukaii xabeh akaso hudu Tom kodaya basuyi xabe aka dauke network wanda sukah setah karfe biyu da rabi sbd munah dayawa sosaii a maxabarmun dan munkaii 600 hundred ammah wanda sukai basufi 100 hundred bah shine kawaii muh matsalar muh anan kamar kaduna ikara lga kuya ward tashar Ango 005

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here