Hukumar tattara sakamakon zabe ta kasa (INEC) ta dage zamanta zuwa gobe Litinin 27 ga Fabrairu, 2023 da karfe 11 na safe.
In za ku tuna cewa Cibiyar ta bude karbar sakamakon zabe a hukumance ne da misalin karfe 1 na yammacin ranar Lahadi kuma ta tafi hutu bayan ta zauna kasa da mintuna 30 a in da da misalin karfe 6 na yamma ta dage zamanta zuwa ranar litinin domin babu wani sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya Abuja da ya zo mata.
Shugaban masu tattara kuri’a na tarayya, wanda kuma shi ne shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ci gaba da zama da misalin karfe 6 na yammacin ranar Lahadi, ya kira jami’in zabe na jihar Ekiti, Farfesa Akeem Lasisi, wanda ya shirya da sakamakon zaben.
Farfesa Lasisi ya gabatar da sakamakon kamar haka:
LP – 11,397
NNPP – 264
PDP – 89,554
Jimlar jefa kuri’a – 314,472
Bayan haka, Farfesa Yakubu ya tambayi ko akwai sauran jami’an da suka kawo sakamako daga Jihohi da babban birnin tarayya Abuja, kuma babu ko daya, shugaban INEC na kasa ya dage zaman har zuwa ranar litinin da karfe 11 na dare, inda ake sa ran cewa wasu sakamakon daga sassan kasar nan za su isa cibiyar tattara bayanai ta kasa. a Abuja.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a yanzu haka ana dakon sakamako daga Jihohi 35 na tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja domin sanar da hukuma.