INEC ta dage ranar karbar sakamakon zaben shugabancin Najeriya

1
103

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta dage ranar fara karbar sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.

INEC ta ce za a fara karbar sakamakon zaben ne da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Litinin, daidai da ranar 27 ga watan Fabrairu.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu, wanda ya bayyana hakan a Abuja, ya ce har yanzu basu fara karbar sakamakon yadda aka gudanar da zabe a jihohin kasar ba.

Rahotanni daga kasar na cewa ‘yan Najeriya na ci gaba da dakon sakamakon zaben shugabancin kasar, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da sanya idanu kan wanda zai maye gurbin shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda ke gab da kare wa’adi na biyu akan mulki.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here