Zaben 2023: INEC za ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasa zuwa karfe 6 na yamma

0
149

Idan dai za a iya tunawa dai an bude cibiyar da misalin karfe 1 na ranar Lahadi sabanin karfe 12 na rana wanda shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar a ranar Asabar.

Shugaban INEC, Farfesa Yakubu, ya bayyana rashin samun sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya (Abuja) a matsayin dalilan dage bayyana sakamakon.

Yakubu ya ce da karfe 6 na yamma ana sa ran cewa wasu sakamakon za su isa cibiyar tattara bayanai ta kasa INEC domin sanar da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here