Atiku Abubakar ya samu nasara a jihar Yobe

0
112

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a jihar Yobe ranar Asabar.

 

Sakamakon zaben da aka tattara daga kananan hukumomi 17 na jihar ya nuna cewa Atiku ya samu nasara da kuri’u 198,567 yayin da shi kuma Tinubu ya tashi da kuri’u 151,459.

 

Da yake ayyana sakamakon zaben, babban baturen tattara sakamakon, Farfesa Umaru Pate, ya ce, dan takarar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya samu kuri’u 18,270 da ya zo na uku a zaben.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here