Atiku ya lashe Adamawa da kuri’u 417,611

0
91

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban kasa a Jiharsa ta Adamawa.

Sakamakon da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar ya nuna Atiku, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’yyar adawa ta PDP, ya yi nasara a 20 daga cikin kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar.

Sakamakon zaben ya nuna, Atiku ya samu kuri’u 417,611, sai Tinubu na APC day a samu kuri’u 182,881.

Ragowar jam’iyyu da suka hada da A 654, AA 536, AAC 646, ADC 3,398, ADP 1,906, APGA 887, APM 650, APP 372, BP 522, LP 105,648, NNPP 8,006, NRM 1563, PRP 701, SDP 1,944, YPP 958 da kuma ZLP da ta samu kuri’u 2,257.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here