Hedikwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ci gaba ta karba da kuma bayyana sakamakon shugaban kasa bayan ta dakatar da aikin a ranar Lahadi da dare.
An ci gaba da aikin ne a Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa da ke Abuja, karkashin jagorancin shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda shi ne baturen zabe na kasa.
A zaman da ka ci gaba a safiyar Litinin ake sa ran karbar sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohi 35 da kuma Birnin Tarayya.
Idan ba a manta ba an dage zaman ne daga ranar Lahadi bayan da INEC ta karbi sakamakon zaben shugaban kasa na Jihar Ekiti.
Ana sa ran bayan nan ne za a sanar da wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu 2023.
Jam’iyyu hudu ne ake gani suna kan gaba a zaben shugaban kasar wanda shi ne karo na bakwai daga lokacin da Najeriya ta sake dawowar Najeriya kan tsarin mulkin dimokuradiyya shekarar 1999.