Wadanda sakamakon zabe bai yi wa dadi ba sun kai wa ’yan kasuwa hari a Legas

0
125

Wasu ’yan daba dauke da makamai da ake kyautata zaton wadanda sakamakon zabe bai yi wa dadi ba ne sun kai farmaki wasu kasuwannin Jihar Legas.

Kasuwannin da aka kai wa harin sun hada da ta kayan safaya ta Ladipo da kasuwar Ebute-Ero da kuma ta Balogun.

Sun dira kasuwannin ne wajen misalin karfe 10:00 na safe, inda suka rika farmakar ’yan kasuwar.

Sakamakon zaben Jihar ta Legas dai ya nuna dan takarar LP, Peter Obi ya sha gaban na APC, Bola Tinubu, wanda tsohon Gwamnan na Legas ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here