INEC ta dage ci gaba da tattara sakamakon zabe

0
83

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta kara dage ci gaba da tattara sakamakon zaben Shugaban Kasa zuwa karfe 3:30 na yamma.

Kakakin INEC, Festus Okoye ne, ya bayyana hakan a zauren bayyana sakamakon zaben da ke Abuja.

Okoye, ya ce an kara dage lokacin ne domin bai wa sauran jihohi damar kawo sakamakonsu, ta yadda za a iya fadin sakamakon jihohi da dama a lokaci guda.

Tun farko dai an shirya ci gaba da sanar da sakamakon ne da karfe 11 na safiyar yau Talata, sai dai INEC ta sanar da dage sanarwar zuwa karfe 2.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here