Yan sanda sun kama shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya, Alhassan Ado Doguwa

0
92
Hukumar yan sanda ta kama shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Doguwa, saboda zargin kisan wasu magoya bayan jam’iyyar adawa a yankin.
Jaridar SAHELIAN TIMES ta rawaito cewa an kama Doguwa ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano , a kan hanyarsa  ta zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin umarah a ranar talata.
Kamen ba zai rasa nasaba da kisan da aka yi wa magoya bayan ‘yan adawa kusan 15 a karamar hukumar Tudunwada a lokacin zaben da aka kammala ba .
Rahotanni sun ce an kulle wasu daga cikin mutane a wani gini inda aka kona su kurmus, lamarin da ya sa aka gagara kubutar da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here