A yammacin Larabar da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta mikawa zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, takardar shaidar lashe zaben shugaban kasa na 2023 da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Shugaban INEC kuma babban jamiāin tattara sakamakon zabe na tarayya Farfesa Mahmood Yakubu ne ya gabatar da takardar shaidar a cibiyar tattara bayanai ta kasa (NCC) da ke Abuja.
Haka kuma, an baiwa zababben mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima takardar shaidar cin zabe.
Tinubu da Shettima sun kasance tare da matansu a takaitaccen taron da aka fara da misalin karfe 3:30 na rana.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Babagana Monguno (rtd) sun halarci bikin, da wasu jiga-jigan jamāiyyar APC.
Da yake jawabi bayan an ba shi takardar shaidar lashe zaben, zababben shugaban kasa, Tinubu ya ce takardar shaidar ta nuna cewa kowa zai iya cimma wani buri a rayuwarsa in har yayi yakini da imani.
Ya yi alkawarin yin aiki ba dare ba rana tare da iyakar iyawarsa don ganin Najeriya ta gyaru.
Tun da sanyin safiyar ranar ne Farfesa Yakubu ya ayyana Tinubu na jamāiyyar APC a matsayin zababben shugaban kasa, saboda ya samu mafi rinjayen kuriāun da aka kada kuma ya cika sharuddan doka.
Tinubu ya samu kuriāu 8,805,655 inda ya doke babban abokin hamayyarsa kuma dan takarar jamāiyyar PDP, Atiku Abubakar, wanda ya samu kuriāu 6,984,520.
Atiku ya biyo bayan dan takarar jamāiyyar Labour Party (LP), Peter Obi wanda ya samu kuriāu 6,098,798 da kuma Rabiāu Musa Kwankwaso na jamāiyyar New Nigeria Peopleās Party (NNPP) wanda ya samu kuriāu 1,496,687.