Faduwar wata tankar mai ya yi sanadin haddasa gobarar da ta sa mutane a yankin Jere na Jihar Kaduna, tafka asara dukiya mai tarin yawa.
Lamarin ya faru ne a kan babban titin Kaduna zuwa garin Jere a ranar Laraba.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da wakilin watsa labaran Masarautar Jere, Ahmad Abdulkarim Dalhat, ya fitar da safiyar ranar Laraba.
Ya ce gobarar ta yi sanadin konewar shaguna, motoci, gidaje masu tarin yawa.
Ya zuwa yanzu dai ba a tantance adadin dukiyar da aka yi asara ba, sannan ba a samu labarin asarar rai ba.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a jihar, ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba.