Kotu ta tasa kyeyar shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya zuwa gidan yari

0
120

A ranar Laraba ne wata kotun majistare da ke Kano ta tasa keyar shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa gidan yari har zuwa lokacin da za ai belinsa.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa wanda ake kara, Alhassan Doguwa yana fuskantar shari’a kan laifuka da dama da suka hada da, hada baki, kisan kai, mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba, barna da hargitsa jama’a.

Babban Alkalin Kotun, Ibrahim Mansur Yola ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara har zuwa ranar 7 ga Maris , 2023 don sauraron bukatar neman belinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here