Tinubu ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya na 2023

0
96

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 da kuri’a miliyan 8,794,726.

Tsohon matainmakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ne ke biye masa da kuri’u miliyan 6,984,520.

Sai kuma dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi wanda ya samu kuri’a miliyan 6,101,533.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya zo na hudu da kuri’u miliyan 1,496,687.

Idan an jima ne kuma mutumin da ya yi nasarar wato Bola Ahmed Tinubu zai je dakin taron da ake tattara sakamako domin karbar shaidar lashe zaben.

Kusan za a iya cewa wannan ne sakamakon zaben da ya fi kowanne daukar dogon lokacin kafin a sanar da shi a baya-bayan nan sakamakon dalilai da dama.

Jam’iyyun adawa na PDP da LP sun ce ba za su karbi sakamakon ba bisa zargin tafka magudi a mazabu da dama, inda kuma suka ce za su garzaya kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here