Buhari ya nemi alfarmar a zaɓi Dikko Raɗɗa a matsayin gwamnan jahar Katsina

0
104

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya nemi alfarmar yan jihar Katsina tare da kira a gare su da su zaɓi ɗantakarar jam’iyyar APC, Dr. Dikko Raɗɗa a zaɓen gwamnoni dake tafe.

Shugaban ƙasar yayi wannan kiran ne a cikin wani video da a yayin da yake gabatar da jawabi a gidan sa dake Daura.

Buhari ya bayyana Dr. Dikko Raɗɗa a matsayin jagora kuma sananne wanda ya bada gudunmawa a jam’iyyar APC.

Ya kuma bada yaƙinin cewa  kwarewar sa zata kawo cigaba a jihar Katsina.

Buhari yayi kira ga al’ummar jihar dasu kauda duk wani bambanci

dake tsakanin su ta hanyar zaɓen Dikko Raɗɗa wanda yace shine mafi chanchanta.

Haka zalika, shugaban yayi kira da a zaɓi sauran yantakarar yanmajalisar dokoki ƙarƙashin jam’iyyar APC wanda acewar shi hakan zai kawo cigaba a jihar.

Shugaban a cikin jawabin ya ba a’lummar jihar hakuri bisa halin matsi da suka shiga dalilin chanza ƙuɗaɗe.

Buhari yace an chanza ƙuɗaɗen domin karfafa tattalin arzikin kasa ba don wata manufa ba.

Daga ƙarshe yayi godiya ga al’ummar jihar tare da yin fatan za’a yi zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here