Dubun wani mai damfarar Kanawa da sunan hukamar kidaya ta cika

0
145

Dubun wani dan damfara da ke sojan gona a matsayin jamiā€™in Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) yana karbar kudin mutane ta cika a Jihar Kano.

Hukumar ta kama wanda ake zargin ne a Karamar Hukumar Wudil, inda yake amfani da sunanta yana karbar kudaden mutane da sunan zai tabbatar da sunayensu da bayanan gidaje ba su samu matsala ba a aikin kidayar mutane da gidaje da hukumar za ta yi nan ba da jimawa ba.

Mai magana da yawun hukumar, Jamila Abdulkadir, ta shaida wa ā€™yan jarida cewa ā€œWannan hukuma ta nesanta kanta da bayanan da ke yawo na karbar N5,000 don tabbatar da sunan wanda suka cike aikin kidaya na wucin-gadi a Jihar Kano.

ā€œMun yi nasarar damke wani daga cikin masu yin wannan aika-aika a Karamar Hukumar Wudil tare da damka shi ga ā€™yan sanda don gudanar da bincike.

ā€œDa wannan ne hukumar take kara jan hankalin alā€™umma cewa su guji duk wasu da ke karbar kudi don tabbatar da bayanansu kan batun kidaya a Jihar Kano.ā€

Ta kara da cewar, bisa bayanan da ta samu, ta sa jamiā€™an tsaro bincikar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here