Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Tinubu da tawagar sa a Daura

0
101

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin sabon zababben shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashin Shettima a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.

Mataimakin shugaban kasar kan al’amuran shafukan sada zumunta, Bashir Ahmed ne ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce zababben shugaban ya samu rakiyar wasu gwamnonin jam’iyyar APC zuwa gidan shugaban mai barin gado.

Shugaba Muhammad Buhari tare da Bola Tinubu
Shugaba Muhammad Buhari tare da Bola Tinubu © BashirAhmad

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da Bola Ahmed Tinubu ya karbi takardar shaidar lashe zabe da hukumar INEC ta mika masa da yammacin ranar Laraba, tare da mataimakinsa Kashim Shettima a Abuja, babban birnin kasar.

A ranar 25 ga watan Fabrairu ne aka gudanar da zaben shugaban kassa da na ‘yan majalisun tarayya a sassan Najeriya, zaben da ya ja hankalin shugabannin kasashen duniya.

Daga cikin gwamnonin da suka yiwa zababben shugaban rakiya akwai, Mallam Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna, gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar, da tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari.

Tawagar Bola Tinubu a gidan shugaba Buhari da ke Daura
Tawagar Bola Tinubu a gidan shugaba Buhari da ke Daura © BashirAhmad

Sauran sun hada da shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Abdullahi Adamu, da gwamnan jihar Zamfara na yanzu, Bello Matawalle, da takwaransa na jihar Legas Sanwo Olu, da kuma Simon Lalong na jihar Filato da dai sauransu.

Wasu daga cikin gwamnonin APC kenan da suka yi wa zababben shugaban rakiya
Wasu daga cikin gwamnonin APC kenan da suka yi wa zababben shugaban rakiya © BashirAhmad

Najeriya dai na daya daga cikin kasashen Afirka da ke da karfin tattalin arziki da kuma yawan jama’a.

Rahotanni daga kasar sun ce sama da mutum miliyan 90 suka. karbi katin zabe, gabanin fara babban zaben kasar.

Bola Ahmed Tinubu dai ya kada abokan hamayyar sa da dama, ciki kuwa har da Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDp, sai Peter Obi na jam’iyyar Labou da kuma Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP.

Jam’iyyun adawa da dama ne suka kalubalanci sakamakon zaben, musamman jam’iyyun PDP da na Labour da suke zargin an tafka magudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here