Hukumar kashe gobara ta Kano ta ceci ran mutum 46 da kubutar da dukiyar Naira miliyan 95.4 cikin wata 1

0
101

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta ceci rayukan jama’a da dukiyoyin 46 da kudinsu ya kai Naira miliyan 95.4 daga gobara 82 da aka samu a cikin watan Fabrairu.

Hukumar ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya fitar ranar Juma’a a Kano.

Abdullahi ya bayyana cewa mutum 8 ne suka rasa rayukansu, yayin da gobara ta lalata dukiyoyin da suka kai na Naira miliyan 31.8.

“Mun amsa kiran ceto 35 da amsa kiran ƙarya 13 daga mazauna jihar,” in ji shi.

Kakakin ya shawarci mazauna garin da su rika kula da gobara domin gujewa hasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here