Jami’an tsaro sun dakile harin da aka kai banki a Taraba

0
101

Jami’an tsaro sun dakile harin da aka kai wa wani bankin kasuwanci biyu a garin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba.

Hatsaniyar ta taso ne bayan wasu sun daga kara cewa wasu almajirai biyu a layin Hammanruwan Way sun mutu bayn sun ci abincin sadaka da wata mata ta ba su.

A kan haka ne wasu bata-gari suka yi zuga suka bi matar, ita kuma ganin haka ta tsere ta shiga cikin bankin kasuwanci, domin tsira da rayuwarta.

Matasan sun tsaya kai da fata sai an miko musu ita ko su shiga bankin da karfin tsiya, inda suka fara farfasa injinan cirar kudi na ATM biyu da ke bankin na Untiy.

Ganin haka ne aka yi wa sojoji da ’yan sanda kiran neman dauki, kuma ba a jima ba, suka kawo dauki tare da tarwatsa matasan.

Sai dai kafin zuwansu, matasan sun farfasa injinan cirar kudi na ATM biyu da ke bankin Untiy.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya musanta cewa almajirai biyu sun mutu bayan cin abincin sadaka matar ta ba su.

Ya ce matar ta bai wa almajiran abinci, amma ba su kai g ci ba, saboda allurai da ake zargin sun gani a cikin abincin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here