John Markus Ayuba: Wane ne mataimakin dan takarar gwamnan PDP a jihar Kaduna?

0
76

Dokta John Markus Ayuba, shi ne Shugaban masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar PDP a Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna, kuma ya kasance malamin jami’a, gogaggen ma’aikacin banki kuma kwamishinan kudi wanda ya ba da gudummawa sosai ga Jam’iyyar PDP a jihar.

Farkon rayuwarsa

An haifi John Markus Ayuba a ranar 15 ga Mayu, 1958 a Kudancin Jihar Kaduna.

Ya halarci Makarantar Firamare ta St. Anthony Mabushi Kataf daga 1965 zuwa 1971.

Mahaifin John Markus Ayuba ya rasu a shekarar 1969, yana dan shekara 4 kacal a duniya, lokacin yana makarantar Firamare.

Ya yi karatunsa na Sakandare a 1976 a makarantar St. Joseph’s Seminary da ke Zariya, inda ya zamo dalibi mafi hazaka a ajinsu.

Ayuba ya zarce zuwa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi digirinsa na farko a fannin Gudanar da Kasuwanci (Business Administration), inda ya zama mafi hazakar dalibi a shekara 1980.

John Markus Ayuba ya sake yin digirinsa na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a shekarar 1982.

Kazalika ya sake halartar Jami’ar a shekarar 1999 inda ya yi karatun digirinsa na uku wato (Ph.D) ya kammala a matsayin Dokta.

Ya yi kwasa-kwasai da dama a jami’o’i gida da wajen Najeriya da suka hada da Jami’ar Harvard, Jami’ar Boston, Jami’ar Hammersmith da ke Landan da sauransu.

Rayuwar aikinsa

Ayuba ya fara aiki da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a matsayin mataimakin Lakcara na I.

Daga bisani ya sauya shekar aiki zuwa kamfanoni masu zaman kansu a 1988, inda ya fara aiki a matsayin Manajan kamfanin UTC (Nig.)

Ya samu karin girma zuwa Manaja sannan daga baya aka nada shi a matsayin Manajan yanki a Kano a shekarar 1989.

A watan Yuli 1989, ya koma ICON Ltd (Bankin Kasuwanci) a matsayin Mataimakin Manaja.

A 1991, ya zama Manaja mai kula da bayar da lamuni na gama-gari.

An daga matsayinsa zuwa Babban Manajan zuba jari na bankin a 1993 zuwa 1996.

A 1996, an nada shi Babban Manaja a Bankin Inland (Nig.) Plc.

Daga bisani ya zama Mataimakin Janar-Manaja da shugaban rukunin Bankin a 1998.

A shekara ta 2001, an kara masa girma zuwa Mataimakin Janar-Manaja.

A watan Disamba 2003, an bai wa Dokta Ayuba mukamin Janar-Manaja, na Bankin Zuba Jari, na Lion Bank of Nigeria Plc.

Sannan ya kasance Babban Darakta na Bankin Zuba Jari, inda ya ci gaba da jan ragamar bankin.

A watan Oktoba 2005, an nada shi a matsayin Shugaban Sashen Kasuwanci na Bankin Diamond Plc, bayan an hade bankin da Lion of Nigeria Plc.

Dokta Ayuba Kirista ne kuma mabiyin darikar Katolika wanda aka horar da shi a makarantun mishan tun daga firamare zuwa matakin sakandare.

Ya yi hidimar coci a wurare daban-daban tun yana karami tare da kakanninsa a cocin Katolika irin su Cocin Katolika ta Maria Assumpta, Cocin Mabushi Kataf da St. Augustine Hippo.

Ya zama shugaban Cocin Kongo Campus, da ke Zariya a 1988.

Ya zama mai bada shawara a Cocin Anthony Parish, da ke Gbaja Surulere a Jihar Legas daga 1997-1999.

Iyalan Dokta Ayuba

Ayuba ya auri Deborah John a ranar 2 ga Oktoba, 1982, kuma Allah Ya albarka ce da samun karuwar ’ya’ya guda uku, mata biyu da namiji daya; Patience, Gloria da kuma John.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here