‘Yan sanda sun tabbatar da kisan gillar da a ka yiwa mahaifin shugaban karamar hukuma a Kano

0
92

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da kisan gillar da aka yi wa hakimin kauyen Maigari, karamar hukumar Rimin Gado ta Kano.

An ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka kashe Alhaji Dahiru Abbas mai shekaru 70 a gidan sa ranar Lahadi.

An ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka kashe Alhaji Dahiru Abbas mai shekaru 70 a gidan sa ranar Lahadi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

“A ranar Lahadi da misalin karfe 3:05 na safe ne aka samu rahoton cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki gidan Abbas Hakimin Kauye Maigari, karamar hukumar Rimin Gado a kokarinsu na yin garkuwa da shi.

Wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a cikin lamarin sun harbi shugaban kauyen a kirji, inda aka garzaya da shi asibitin kwararru na Murtala Muhammed Kano inda ya mutu a lokacin da yake karbar magani,” inji shi.

Haruna-Kiyawa ya kara da cewa an kara zage damtse domin kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika yayin da tawagogin ‘Operation Restore Peace’ suka fara kai dauki.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa marigayi Abbas shi ne mahaifin shugaban karamar hukumar Rimin Gado, Munir Dahiru-Maigari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here