Bankuna sun fara mayar wa ‘yan Najeriya tsoffin takardun Naira

0
262

Biyo bayan hukuncin da kotun kolin Najeriya ta yanke, wanda ya kara wa’adin dokar amfani da tsohon kudi zuwa watan Disamba, wasu bankunan ajiya sun fara biya da tsoffin takardun kudi.

Binciken da jaridar Daily Trust ta gudanar, ya nuna cewa wasu bankunan kasuwanci a birnin Kano da Abuja sun fara bawa jama’a tsofaffin takardun kudi na Naira 500 da kuma 1000.

Yayin da wasu rassan bankin Guarantee Trust Bank (GTB) suka fitar da tsoffin takardun kudin, wasu kuma kamar bankin Polaris da ke Abuja ba su fara ba har yanzu.

Majiyoyi daga bankin GT sun ce sun sami umarni daga hukumominsu kan su fara bawa jama’a tsoffin takardun kudi.

Masana harkokin tattalin arziki sun bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya umurci gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele, da ya yi biyayya ga hukuncin da aka yanke kan ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudin har zuwa watan Disambar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here