Jam’iyyar NNPP ta nemi hadewa da wasu jam’iyyu

0
114

Jam’iyyar NNPP ta yi kira ga mambobinta da ‘yan takararta kan kulla yarjejeniyar hada kai da kowace jam’iyyar siyasa domin lashe zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi.

Jam’iyyar ta yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Mista Agbo Major, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

Major ya shawarci ‘ya’yan jam’iyyar da su mai da hankali, su kuma zage damtse wajen yakin neman zabe tare da tabbatar da cewa sun kammala zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a gudanar a ranar 11 ga watan Maris a fadin kasar nan.

Major ya ce hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi wa NNPP rajista a shekarar 2002 kuma jam’iyyar tana kara samun nasara da fadada iyakokinta a fagen siyasar kasar a kowace da’irar zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here