Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da belin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa kan kudi naira miliyan 500, wanda aka gurfanar da shi a gaban wata kotun majistare bisa zargin kone-kone da kisa.
‘Yan sanda sun kama Doguwa a Kano sakamakon rikicin da ya yi sanadin mace-mace da kone-kone a karamar hukumar Tudun Wada a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu .
An gurfanar da dan majalisar a gaban kotun majistare tare da wasu laifukan hada baki, kisan kai, konewa, da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da dai sauransu.
Sai dai lauyan wanda ake tuhuma Nureini Jimoh (SAN) ya bukaci mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa ya bayar da belin wanda ake tuhuma bisa laifin tauye hakkinsa da kuma rashin hurumin da kotun majistare na tsare shi.
Jimoh ya kara da cewa tun da kotun ba ta da hurumin tuhumar wanda ake tuhuma da laifin kisan kai da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, kotun majistaren ba ta da hurumin ci gaba da tsare shi Doguwa.
Mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa da ya saurari bukatar, ya bayar da belin da sharadin cewa wanda ake tuhuma ya bayar da mutum biyu wadanda za su tsaya masa, daya daga cikinsu ya kasance basarake mai daraja ta daya, dayan kuma ya kasance babban sakatare a ma’aikatan gwamnatin tarayya ko na jiha.
Alkalin kotun ya umarci wanda ake zargin da ya ajiye takardun tafiye tafiyensa a wurin rajistaran kotun, wadanda za a iya fitar da su idan ana bukatar tafiya. Dole ne a sake gabatar da takaddun bayan dawowa daga tafiya.
Kotun ta kuma ce dan majalisar kar ya ziyartarci mazabar sa a yayin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da ke tafe.