Ba za mu bari NNPP ta yi magudin zabe ba a Kano — Gwamnatin Kano

0
99

Gwamnatin jahar Kano karkashin jam’iyyar APC ta sha alwashin tabbatar da hana duk wani yunkuri da ‘yan adawa za su yi na yin magudi a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jaha da za a gudanar a jahar, a ranar 11 ga watan Maris.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jahar, Malam Muhammad Garba, ya fitar ranar Litinin a Kano.

Ya ce dole ne gwamnati ta jawo hankalin jama’a “saboda hakan na iya kawo cikas ga zaben gwamna da na ‘yan majalisun da za a yi.

Ya kuma kara da cewa gwamnati ta samu sahihin bayanai kan yadda za a dauki ‘yan baranda daga kauyukan Kano da wajenta domin tada zaune tsaye a zaben ta hanyar tashin hankali, magudin zabe, kwace akwatuna da kone-kone.

Garba ya kara da cewa, a shekarar 2019 ‘yan adawa sun gudanar da wani shiri na magudin zabe, musamman a kananan hukumomi, inda matasa, wadanda galibi ba su da katin zabe, suka daura damarar yin aika-aika.

Kwamishinan ya yi zargin cewa a wannan karon ‘yan adawa na shirin kawo hargitsi ta hanyar amfani da ‘yan baranda don tayar da tarzoma da nufin tarwatsa masu kada kuri’a a rumfunan zabe domin samun damar yin magudin zabe da kuma karkatar da ra’ayin jama’a.

Ya kuma yi zargin cewa sanarwar da ‘yan adawa a jihar suka fitar wasa ne kawai amma sun kammala munanan shirye-shiryensu na ganin sun kawo cikas a harkar zabe tare da tayar da tarzoma.

Sai dai Garba ya ba da tabbacin cewa gwamnatin APC za ta tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a jahar.

Kwamishinan ya yi kira ga jami’an tsaro da abin ya shafa da su kasance cikin shiri don sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ta hanyar kama duk wani mutum ko wata kungiya da ke da niyyar tayar da fitina don hana mutane yin amfani da ikonsu.

Leadership Hausa ya rawaito cewa babbar jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar, a ranar Litinin ta sanar da mazauna jahar ta hanyar wani taron manema labarai kan shirin da jam’iyyar APC mai mulki ta yi na murza tsarin dimokuradiyya ta hanyar tsoratar da masu zabe.

Don haka jam’iyyar NNPP ta bukaci hukumomin tsaro da su samar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar jaha cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da tashin hankali ba.

Wani jigo a jam’iyyar, Dokta Bappa Bichi, ya shaida wa manema labarai cewa, muradin ‘yan Nijeriya na zaben shugabannin da suke so ba zai yiwu ba idan hukumomin tsaro suka kasa samar da daidaito ga dukkanin jam’iyyun siyasa.

A cewarsa, hakan zai ba da damar gudanar da zabe na gaskiya da adalci.

Bichi ya kuma bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da hukumomin tsaro da su kasance a tsaka-tsaki da adalci da kuma rashin nuna banbanci wajen gudanar da ayyukansu a lokutan zabe da kuma bayan zabe.

A baya dai rundunar ‘yansandan jihar ta gargadi jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu da magoya bayansu kan duk wani tashin hankali.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya kuma bayar da tabbacin ba za su dauki bangare a zaben ba.

A cewarsa, hukumomin tsaro sun kuduri aniyar tabbatar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da kama tare da hukunta wadanda suka tada tarzoma kamar yadda aka yi a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here