Ganduje ya yi wa fursunoni 12 afuwa kwanaki uku kafin zabe

0
83

Kwanaki uku kafin zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokoki, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya yi afuwa wa wasu fursunoni 12 da aka tabbatar wa hukuncin kisa kuma tuni shida daga cikinsu an zartar musu da hukuncin daurin rai da rai.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Yari (NCS) reshen Jihar Kano, SC cewar SC Lawan, Ganduje ya kuma yi afuwa ga wasu fursunoni mata guda hudu da ke cin sarka ta tsawon lokaci bayan samunsu da kyawawan dabi’u kamar yadda Hukumar NCS din ta bayar da dama.

Kazalika, Ganduje ya bai wa fursunonin da ya ’yantar kyautar naira dubu biyar-biyar domin su yi guzurin komawa gida wajen ’yan uwansu.

Jami’in ya ce Shugaban Kwamitin Yi wa Masu Laifi Afuwa, Abdullahi Garba Rano da kuma Kwanturolan Gidajen Yarin Kano, Sulaiman Muhammad Inuwa, sun yaba wa Ganduje dangane da yadda ya ribaci ikon da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya ba shi na ’yantar da fursunonin da aka samu da halayya ta gari yayin zamansu a gidan kaso.

“Inuwa ya bayyana ’yantattun fursunonin a matsayin jakadu nagari na Gidajen Yarin Najeriya. Yana kuma gargadinsu da su kauracewa fadawa cikin duk wani laifi da ka iya mayar da su inda suka fito. ”

Bayanai sun ce wadansu daga cikin ’yantattun fursunonin sun shafe fiye da shekaru 25 suna jiran a zartar musu da hukunci.

A wata tattanawa da nadar murya da aka yi da wasu daga cikinsu, wani mai shekara 69, ya ce ya shafe fiye da shekaru 23, amma a yanzu babu abin da zai yi face godiya ga gwamna da kuma mahukuntan gidan gyaran halin da suka yi ruwa da tsaki wajen ’yantar da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here