INEC na son kotu ta sauya izinin da ta bai wa Atiku da Obi

0
92

Hukumar Zaben Najeriya, INEC ta bukaci kotun da ke sauraren korafin zaben shugaban kasa da ta sauya izinin da aka bai wa Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour na nazartar kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben shugaban kasa na 2023.

A wani kudiri  da ta fitar a ranar 4 ga wannan wata na  Maris, INEC ta yi fatan kotun za ta sauya umarnin wucen-gadi da ke hana ta taba kayayyakin zaben, tana mai cewa, akwai bukatar ta sake seta na’urar BVAS domin gudanar da zaben gwamnonin johohin Najeriya a wannan Asabar mai zuwa.

A ranar 3 ga watan nan ne, kotun daukaka karar ta bai wa Atiku Abubakar da Peter Obi damar nazartar na’urar ta BVAS da INEC ta yi amfani da ita a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan jiya.

Kotun ta hana INEC ta’ammuli da na’urar har sai ‘yan takarar biyu sun gudanar da binciken kwa-kwaf a cikin na’urar biyo bayan zargin da suka yi na yi musu magudi a zaben.

‘Yan takarar biyu,  sun shigar da kara ne bayan sun fadi zaben, inda suka sha kashi a hannun Bola Ahmed Tinubu da INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Yanzu haka INEC ta ce, lallai akwai bukatar da a tura kwararrun injiniyoyin ta akan lokaci domin fara seta na’urar  karkashin shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnoni, tana mai cewa, in ba haka ba, to akwai yiwuwar dage zaben na gwamnoni kamar yadda wata majiya ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here