Lauyoyi sama da 50 ne ke shirin kare nasarar Tinubu yayin da Atiku, Peter Obi suka kai kara kotu

0
107

Akalla lauyoyi 50 ne suka yi tayin kare nasarar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu a kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.

A ranar 1 ga Maris, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Ya samu kuri’u 8,794,726 inda ya doke Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour wanda ya samu kuri’u 6,984,520 da 6,101,533.

Sai dai Atiku Abubakar, Peter Obi, da sauran su sun yi watsi da sakamakon, inda suka zargin an musu magudi  sun kuma sha alwashin kai kokensu zuwa kotu.

Bayan haka, wasu lauyoyin sun nuna sha’awarsu ta kare hakkin Tinubu a kotu kuma a halin yanzu suna jiran karar da Atiku da Obi za su shigar.

Wasu manyan lauyoyin da ke kare wa’adin Tinubu sun hada da Wole Olanipekun Akin, Olujimi Yusuf Ali, Lateef Fagbemi, AU Mustapha, Ahmed Raji, Abiodun Owonikoko Kemi Pinheiro, Niyi Akintola.

Sauran sun hada da HM Liman, Taiwo Osipitan, Babatunde Ogala, Roland Otaru, James Onoja, Muiz Banire, Olusola Oke, Mohammed Abubakar, da dai sauransu.

A halin da ake ciki, Atiku Abubakar ya jagoranci wasu jiga-jigan jam’iyyar wajen gudanar da zanga-zanga a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Shugabannin jam’iyyar PDP sun isa Legacy House, hedikwatar jam’iyyar, da misalin karfe 11 na safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Maris, yayin da wasu amintattun jam’iyyar suka tare su.

Da misalin karfe 11:10 na safe ne aka fara tattakin da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu da sauran ‘yan kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here