Jam’iyyar NNPP ta bakin wani jigonta, Baffa Bichi ta ce suna sane da shirin da gwamnatin Ganduje ta yi na kawo bakin ’yan daba daga kasashen Nijar da Chadi cikin jihar don ganin sun tayar da tarzoma tare da kawo cikas a zaben gwamna da ke tafe.
Dokta Bichi ya kara da cewa, Gwamna Ganduje bai tsaya a nan ba, sai da ya yi kokarin ganin ya yi afuwa ga wasu kasurguman ’yan daba a jihar wadanda aka yanke musu hukuncin kisa don su yi masa aiki a ranar zaben.
“Gwamnatin Kano ta yi afuwa ga tantiran ’yan daba wadanda ke zaman jiran sakamakon yanke musu hukuncin kisa.
“Haka kuma tana kokarin fito da wasu ’yan dabar da ke wasu gidajen yarin a fadin kasar nan.
“Babban misalin shi ne yadda ta fito da wani mai suna Muhammad Abbas mai lambar kurkuku K/35c/2008 daga gidan kurkuku na Jihar Neja.
Sai dai Kwamishinan Labarai na Kano, Muhammad Garba, ya musanta zargin yana mai cewa Ganduje ya yi fursunonin afuwa ne ba da wata manufa ba face ribatar ikon da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya ba shi na idan bukatar hakan ta taso.
Kwamishinan ya kara da cewa, jam’iyyar NNPP na wannan zargin ne kawai saboda fargabar ba za ta yi nasara ba a zaben gwamna da na ’yan majalisar dokoki da za a gudanar a karshen wannan mako.
Ana iya tuna cewa, a wata hira da Ganduje ya yi da Gidan Talabijin na Trust a shekarar 2021, ya bayyana cewa gwamnoni na tsoron sanya hannu kan hukuncin kisa ga wadanda aka yankewa hukuncin “saboda ba sa son a aiwatar da hukuncin kisa daga baya kuma suka gano wanda aka zartarwa hukuncin bai cancanci hakan ba.”