Rashin kulawa ya sa wata mata neman kotu ta raba aurenta da mijinta

0
119

Wata kotu da ke zamanta a yankin Kubwa a Abuja ta raba auren shekara 12 tsakanin wata mata mai suna Amina Hamisu da mijinta, Ibrahim Isyaku, saboda rashin kulawa.

Alkalin kotun, Malam Yahaya Sheshi, ya raba auren ne kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada bayan Amina ta bukaci a raba auren saboda watsi da mijinta ya yi da ita.

Alkalin ya ce, idan aka yi la’akari da hujjojin da shaidu biyu; Mustapha Abdulrasheed da Hadiza Garba suka bayar, magidancin da ake kara ya yi sakaci wajen kula da iyalinsa.

Tun da farko, matar ta shaida wa kotun cewa mijin nata ba ya samar wa iyalinsa da abinci, matsuguni, sutura da magani.

Da yake bayar da shaida, surukin matar, Abdulrasheed, ya ce, da farko mijin ya watsar da matarsa ​​da ’ya’yansa a wani kauye da ke Kano, inda daga baya ’yan uwanta suka nemi ta biyo shi Abuja inda yake da zama.

Ya ce, “Duk da Amina ta biyo shi, mijinta bai canja ba; Iyayenta sun nemi ta koma gidan ’yar uwarta ko zai sauya amma babu abin da ya sauya.”

Abdulrasheed ya kara da cewa wanda ake kara ya kuma raina iyayen matarsa, ​​inda ya goyi bayan kotu da ta raba auren tunda ba shi da muradin ci gaba da zama da ita.

 

Duk da cewa wanda ake karar ya musanta zargin da ake masa, alkalin kotun ya raba auren.

Sannan ya umarci Amina da ta yi iddar wata uku kamar yadda addinin Musulunci ya tanada kafin ta yi sabon aure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here