Tinubu ya bukaci kotu ta ba shi damar duba kayayyakin zabe

0
98

Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da ke zamanta a Abuja, da ta ba su damar duba wasu muhimman kayyakin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta kasa ta yi amfani da su wajen gudanar da zaben shugaban kasa da ya gudana a 25 ga Fabrairun 2023.

 

Tinubu, ta bakin lauyansa, Akintola Makinde, ya ce suna bukatar dubawa da kuma yin kwafin wasu daga cikin takardun zaben domin fara shirye-shiryen tunkarar kare nasarar da Tinubu ya samu a zaben.

“Kayayyakin da muke bukata, za su taimaka wajen sanin hanyar da zamu bi don kwatanta sakamakon da ke cikin rumbun adana bayanai na yanar gizo na INEC da na takardu” in ji Makinde.

Har ila yau, a zaman kotun, Kotun ta ce za ta sake yin duba kan bukatar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gabatar na neman kotun ta sauya umarnin da ta bai wa Jam’iyyoyin Labour LP da Jam’iyyar PDP na basu damar duba kayayyakin da akayi amfani da su wajen gudanar da zaben shugaban kasa na 25 ga Fabrairun, 2023.

 

Kwamitin mutum uku na Kotun daukaka kara ya tsayar da ranar da za su yanke hukunci a kan lamarin bayan sauraron muhawarar bangarorin da abin ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here