Tinubu ya yi Allah wadai da harin Zamfara da Kano

0
109

Bola Ahmed Tinubu, zababben shugaban kasa ya bayyana cewa ‘yan fashi, ta’addanci da tashe-tashen hankali bai kamata su samu wurin zama a Najeriya ba.

Ya bayyana ra’ayinsa ne kan hare-haren da ‘yan bindiga da mahara suka kai a karamar hukumar Maru a jahar Zamfara a karshen mako da kuma garin Maigari da ke karamar hukumar Rimin Gado a jahar Kano.

Tinubu ya bayyana cewa an kashe jami’in ‘yan sanda da dan banga a harin da ‘yan bindiga suka kai a Zamfara.

“A harin na Kano, ‘yan bindiga sun kutsa gidan wani basarake inda suka harbe shi har lahira,” in ji zababben shugaban kasar.

Ya kara da cewa harin da aka kai garin Maru bayan an samu zaman lafiya a Zamfara, ya kara da cewa akwai bukatar a kara kaimi domin murkushe ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda gaba daya.

“A matsayinmu na kasa dole ne mu hada kai domin mu fatattaki wadannan ‘yan ta’addanci gaba daya. Kashe-kashen rashin hankali da ta’asa irin wannan bai kamata su kasance a kasarmu ba,” in ji shi.

Ya jajantawa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mista Usman Baba, da gwamnatin Zamfara da iyalan jami’an tsaron da abin ya shafa game da rasuwar.

Tinubu ya kuma bukaci a gudanar da bincike kan kisan Hakimin Maigari a jahar Kano, wanda shi ne mahaifin Shugaban karamar Hukumar Rimin Gado, Mista Munir Maigari.

Ya mika ta’aziyyarsa ga shugaban karamar hukumar, da gwamnatin jahar Kano da kuma iyalan marigayin bisa mummunan kisan da aka yi wa shugaban al’umma.

A cikin sakon ta’aziyya daban-daban, zababben shugaban kasar ya jajanta wa malamin nan Sheikh Ahmad Gumi da ya rasa mahaifiyar sa da kuma iyalan marigayi Janar Sani Abacha bisa rasuwar dan su Abdullahi.

“Akwai kuma rabuwa da masoyi komai yanayi da shekaru.

“Ba za mu iya tambayar Allah ba, sai dai kawai mu yi addu’a Allah Ta’ala ya jikan su, ya kuma ba mu karfin jure wa rashin su, amin.” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here