Zaben Gwamnoni: Ba mu yi hadaka da kowace jam’iyya ba – LP

0
75

A yayin da ake shirin yin zaben gwamna da ‘yan majalisun dokiki a ranar 11 ga watan Maris na 2023, jam’iyyar LP ta shelanta cewa, ba ta yi hadaka da ko wacce jam’iyya ba

Shugabanta na kasa Barista Julius Abure ne, ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar, inda ya ce, fayyace hakan ya zama wajibi kamar yadda wasu ‘yan siyasa ke yada cewa LP ta yi hadaka da wasu jam’iyyu domin ‘ya’yan jam’iyyarmu su zabe su a zaben da ke tafe.

Julius ya ci gaba da cewa, ba za mu yi wani sake ba wajen ganin ‘yan takararmu na gwamna da kuma na ‘yan majalisun dokoki sun lashe zabuka.

Shugaban ya kuma bai wa miliyoyin masu kada kuri’a da suka yi imani da takarar Peter Obi da kada su karaya, amma su fito su zabi ‘yan takarar gwamna a LP da na ‘yan majalisun dokoki a duk inda suke a kasar nan.

Ya kuma yi kira ga daukacin magoya bayan jam’iyyar LP a fadin kasar nan su fito a cikin kwanciyar hankali da lumana a ranar asabar don zabar ‘yan takarar LP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here