Kwankwaso ya musanta taya Tinubu murnar lashe zabe

0
93

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Engr. Rabiu Kwankwaso ya musanta cewa ya taya Asiwaju Bola Tinubu murna bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana shi a matsayin zababben shugaban kasa.

A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar NNPP, Dr Agbo Major, ya fitar a jiya, Kwankwaso ya ce bai taya tsohon gwamnan Legas murna ba saboda zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu yana da kura-kurai sosai da kuma takaddama.

Ya ce: “Jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP da dan takarar shugaban kasarta, Engr. Rabiu Kwankwaso ba su taya jam’iyyar All Progressives Congress, APC, da dan takararta Asiwaju Bola Tinubu, murnar zabubbukan shugaban kasa da aka yi da kura-kurai da rigima da takaddama ba.

“Rahoton cewa Engr. Kwankwaso ya taya Tinubu murna ne a matsayin zance ne na masu adawa da dimokuradiyya, ‘yan siyasa da ’yan jarida suna yin amfani da farin jinin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

“NNPP ta ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, saboda bai nuna so, fata da kuma wajabcin ’yan Najeriya da suka fito kada kuri’a ba amma sun ji takaicin gazawar INEC wajen gudanar da sahihin zabe da kuma cika mu su alkawarin da ta yi na shigar da sakamakon rumfunan zabe a tashoshinta, wanda zai tabbatar da sahihancin sakamako da bayyana wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

“Abin takaici, zaben shugaban kasa ya zama abin ban mamaki saboda ya kasa cimma burin ‘yan Najeriya da kasashen duniya. 

“NNPP ta kasance makasudin wadannan ‘yan fashin zabe da ke son halin da ake ciki ya ci gaba da kasancewa a matsayin sabuwar Najeriya da jam’iyyar ta yi alkawari idan aka zabe shi.

“Duk masu son mulkin dimokuradiyya da bin doka da oda, za su jira a tantance koke-koken zabe a kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here