Mata miliyan 7 masu juna biyu na fama da cutar yunwa a kasashe 12 – UNICEF

0
105

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya koka da karuwar matan da basa samun wadataccen abinci mai gina jiki musamman masu juna biyu da masu shayarwa.

UNICEF cikin wani rahoto da ya fitar ya ce an samu karuwar matsalar da akalla kashi 25 cikin kasashe 13 galibinsu a Afrika da Asiya, tana mai gargadin cewa idan har ba a dauki matakan magance matsalar ba, ko shakka babu za a samu karuwar haifar jarirai masu ciwon yunwa ko kuma Tamow.

Alkaluman da ke kunshe a rahoton na UNICEF ya nuna cewa adadin mata masu juna biyu da masu shayarwa wadanda basa samun abinci mai gina jiki ya karu daga mutum miliyan 5.5 a shekarar 2020 zuwa miliyan 6 da dubu dari 9 a bana.

Rahoton na UNICEF ya alakanta koma bayan da yadda yakin Rasha a Ukraine ya haddasa yunwa musamman a kasashen da suka dogara da ketare ta fannin abinci.

Rahoton na UNICEF ya ce galibin kasashen da wannan matsala ta fi tsananta na sahun wadanda ko dai su ke fama da rikici ko kuma wadanda ‘yan tawaye ko ‘yan ta’adda ke barazana ga tsaronsu.

Cikin jerin kasashen da rahoton ya bayyana a matsayin kan gaba da ke fama da wannan matsala ta yawaitar matan da basa samun abinci mai gina jiki akwai Afghanistan a kan gaba kana Burkina Faso da Chadi da Habasha sannan Kenya da Mali da Nijar sai Najeriya da Somalia tukuna Sudan da Sudan ta kudu sai kuma Yemen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here