Rikicin APC da PDP ya yi sanadiyyar jikkata wasu matasa

0
104

Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa wasu mutane 14 sun samu raunuka daban-daban a kauyen Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri ta jihar, sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC da PDP.

LEADERSHIP ta tattaro cewa rikici ya barke tsakanin bangarorin biyu a lokacin da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Ambasada Sadikue Baba Abubakar ya ziyarci al’umma a wani rangadin yakin neman zabe.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa Duguri mahaifar gwamnan Jihar Bauchi ne mai ci, Bala Abdulkadir Mohammed, wanda kuma shi ne dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan da za a yi a ranar 18 ga Maris.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Muhammed Wakil, ya ce, “A yau (Alhamis), dan takarar gwamna na jam’iyyar APC ya fita wani taro a kauyen Duguri da ke karkashin gundumar Yuli-Yin, Alkaleri. A karamar hukumar, an samu tashin hankali a yayin gangamin inda mutane 14 suka samu raunuka, daga cikin 14 da suka samu raunuka, an kai shida daga cikinsu cibiyar kula da lafiya matakin farko da ke Duguri, an yi masu magani an sallame su.

“Wasu takwas kuma sun samu munanan raunuka, an garzaya da su babban asibitin Alkaleri.

Sauran bakwai din an dauke su ne daga babban asibitin Alkaleri zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin duba lafiyarsu.

“A cikin wadanda aka kai wa harin akwai jami’an tsaro,” in ji kakakin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here