Yadda aka fara zawarcin mukaman siyasa a gwamnatin Tinubu

0
101
Tinubu

Bukatar magoya bayan duk wata jam’iyyar siyasa shi ne su amfana da wani abu a dalilin kasancewar su ‘ya’yan jam’iyyar, musamman ma idan aka ce jam’iyyar ta samu nasarar lashe babban zabe na kasa da aka yi makon ranar 25 ga watan Fabrairu 2023.

Ladar magoya bayan jam’iyyar siyasa wani abu ne na daban akwai bambanci na mukaman siyasa da za a samu,wannan kuma ya danganta ne kan irin gudunmawar daya ko ta ba jam’iyyar,lokacin da take cikin gwagwarmayar neman nasara a zabe ta.

Shi yasa wadanda suka iya magana ke cewa “Kowa Yaci Ladar Kuturu Dole Yake Mai Aski”.“Ko suce Duniya Susar Jaki Ce Idan Ka Sosa Ma Wani Kai Ma Sai Ya Sosa Maka”.
Masu kamun kafa suna bin mabambantan hanyoyi daban- daban ne domin cimma burinsu na samun mukaman siyasa,da suka hada da bi ta hannun Sarakunan gargajiya,manyan ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, da masu fada aji,hakan take kansacewa irin hanyar da mutum ya san zata fishshe shi ita ce yake ko take bi.

Kungiyar ‘yan ‘uwa musulmi mata ta Nijeriya (FOMWAN) ta yi kira da zabebben Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu,da yaba mata kashi hamsin na mukaman siyasa.

Kungiyar ta taya Shugaban kasar da aka zaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima a nasarar da suka samu a zaben Shugaban kasa.

Shugabar kungiyar ta kasa Hajiya Rafiah Sanni,na mika sakon kungiyar gaTinubu wanda wakilin LEADERSHIP na Ilorin Jihar Kwara ya same shi.

Kungiyar ta musulunci ta jinjina wa hukumar zabe mai zaman kanta kan yadda ta aiwatar da sahihai kuma karbabbun zabubbuka a Nijeriya.

Ta yi kira da jam’iyyu da ‘yan takararsu da suke ganin ba ayi masu daidai ba dasu nemi abi masu hakki a kotu,ba mabiyansu su rika yin kalaman da basu dace ba.

Duk da haka dai ta nuna rashin jin dadinta kan la’akarin da tayi na yadda ba ayi wa mata adalci wajen bada mukaman siyasa,ga kuma kujeran da mata suke samu a majalisun kasa, har da wajen mukaman na siyasa.
FOMWAN ta cigaba da bayanin ko jam’iyya mai mulki (APC) da ‘yan adawa babu wadanda zasu buga kirji suce zasu iya samun nasarar cinye rumfar zabensu ba tare da hadin kan mata ba.

“Don haka shi yasa suke kira da zabebban Shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu da mataimakinsa,Sanata Kashim Shettima su bambanta da saura wajen tabbatar da an ba mata da suka cancanta kashi hamsin,daga sassa daban- daban na kasa.

“Yan Asalin Babban Birnin Tarayya Sun Yi Kira Da A Basu Mukamin Minista
Su ma a nasu bangaren ‘yan asalin Babban Birnin Tarayya Abuja sun yi kira da zabebban Shugaban kasa Tinubu ya basu mukamin Minista ga su ‘yan asalin yankin kamar yadda hukunci kotu ya bayyana,idan ya fara aiki a matsayin Shugaban kasa.

‘Yan asalin Babban Birnin Tarayyar a karkashin inuwar kungiyoyin masu zaman kansu da suke kamfen a bangaren Babban Birnin Tarayya, hakanan ma ta bukaci a aiwatar da yin amfani da tsarin tafiyar da mulki na siyasa kamar yadda yake a tsarin mulki na shekarar 1999,wariyar al’umma kan ‘yan Nijeriya wadanda suke ‘yan asalin Babban Birnin Tarayya.

Jagoran kungiyar Ambasada Ayuba Jacob Ngbako, ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da ‘yan jaridu ranar Lahadi ta makon daya gabata a Abuja a madadin ‘yan asalin Babban Birnin Tarayya, yayi kira da Tinubu ya kafa wata Sakatariya a Abuja saboda ‘yan siyasa da masu goyon baya mazauna Babban Birnin Tarayya.

“Bugu da kari suna kira da ayi dokar da zata kula da jin dadin masu Sarautar gargajiya na Babban Birnin Tarayya da gwamnatin da zata hau kan karagar mulki ta Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima,da tsarin bada tallafi na bunkasa tattalin arziki na musamman,saboda mata da matasa na Babban Birnin Tarayya.

Koda -yake Ngbako duk da yake Tinubu bai lashe zaben Babban Birnin Tarayya ba yayi alkawarin zai kafa gwamnati wadda zata tafi da kowa da kowa wajen cigaban siyasar Babban Birnin Tarayyar.

“Kungiyar zata cugaba da tattaunawa, kamun kafa, da duk yin wani abinda ya dace na bi sau da kafa na mulkin gwamnatin Tinubu da Shettima akan bukatar da muka nema daga wurinta.Muna da tabbacin cewa tunda bukata tamu ta cigaban al’ummar Babban BirninTarayya ce,da yardar Allah zamu samu amincewar a karkashin gwamnatin Tinubu da Shettima.

Ya yi kira da duk al’ummar Nijeriya su bada goyon baya da hadin kai ga gwamnatin Tinubu da Shettima wajen gina kasa mai cigaba da albarkar al’umma. “Tare zamu ga karshen dukkan matsaloli da suke damunmu mu kuma kama hanya mafi dacewa saboda kanmu da wadanda zasu kasance bayanmu kamar yadda ya jaddada”.

Shugabannin Arewa Maso Gabas Sun Yi Kira A Kafa Gwamnatin Data Kunshi Kowane Sashe.

Akwai shugabanni karkashin inuwar kungiyar cigaban sashen Arewa maso gabas (NEDA), da suka yi kira da Shugaban kasa mai jiran gado ya kafa gwamanti wadda zata kunshi Nijeriya wajen kallonta ta fuskoki daban – daban, ba tare da yin la’akari da sashe, addini,ko jam’iyyar siyasar da suke yi ba,da zarar an rantsar da shi 29 ga Mayu 2023.
A taron manema labarai data kira ranar Lahadi ta makon daya gabata Bauchi,babban Sakataren gamaiyar kungiyoyin Komrade Bitako Abubakar Umar, ya taya zabebban Shugaban kasa da mataimakinsa, Bola Tinubu da Sanata Kashim Shettima murnar nasarar lashe zabe,inda ya kira nasararsu a matsayin wata alama ce mai nuna cewa Nijeriya da ‘yan Nijeriya sannu a hankali sun fara wayewa inda suka fara bankwana da salon siyasar addini da bangaranci.

Umar ya ce Nijeriya ta’yan Nijeriya ce ba tare da yin wani la’akari da sashe, addini, al’adar gargajiya, kabila, ko irin siyasar da ake goyon baya,inda ya kara jaddada an kammala zaben Shugaban kasa an kuma sanar da wanda ya samu nasara.Koda akwai wadansu abubuwa da suka taso da yadda ake bi domin samun adalci a cikin tsarin mulkin da kowa ya bada tabbacin zai kare da amfani da shi.

Kungiyar tana da mambobi daga Jihohin da suka kungiyar cigaban sashen nasu ta mika godiyarta ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen samar da yanayi mafi dacewa ga hukumar zabe mai zaman kanta,da ta fara gudanar da zabubbukan Shugaban kasa dana ‘yan majalisun kasa a yanayin da yake na zaman lafiya da kaunar juna.

Har’ila yau kungiyar cigaban sashen Arewa maso gabas ta jinjinawa Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Farfesa Mahmud Yakubu saboda yadda ya fara gudanar da zabubbuka,da suka kasance an yi su cikin kwanciyar hankali da lumana, da adalci a tarihin Nijeriya.

NEDA ta cigaba da cewa an yi ma zaben kallon wanda yafi sahihanci bama kamar idan aka yi la’akari da ‘yan adawa sun kada Sanatocin da suke gab da kammala wa’adinsu,suka kasa samun damar a sake zabensa,ya sha bamban da yadda wadanda suke damawar siyasa ke cewa ga hanyar data kamata abi.

Komrade Bitako Abubakar Umar ya kaddada bukatar da ake ta duk ‘yan Nijeriya da suka hada da Dattawa, matasa, mata da yara su cigaba da zama cikin lumana domin neman abinda zai taimaka masu tafiyar da raywarsu.

Ya ce zanga- zangar nuna kyama akan yadda ‘yansanda ke tafiyar da ayyukansu da ake kira da suna EndSARS yakamata ta koyawa ‘yan Nijeriya darasi domin kuwa, kamar yadda ya tunatar yadda ‘yan siyasa suka yi amfani da wadanda suka yi zanga- zangar sune dai suka sake amfani dasu domin cimma burin na zama Shugabanninsu.

“Babu wani dan siyasa,ko masu sa ayi wani abu, ko kungiyar siyasa da ke son yin wani abinda zai iya kawo cikas ga kasa,idan babu mutane Nijeriya sunan kasa ce mai haruffa bakwai,ya dace ace da akwai mutane wadanda sai da sune komai na zamantakewar al’umma ke yiyuwa cikin zaman lafiya kwanciyar hankali da lumana”.
“Mu yi amfani da abinda ya faru mu bullo da hanyar da zata kawo cigaban Nijeriya haka ne Nijeriya zata cigaba da kasancewa dunkulalliyar kasa daya,ba wata bukatar wani dan siyasa da tafi hadin kanta da kasancewa zaman lafiyar al’ummarta”.

Bugu da kari ya ce matsaloli ko bukatu kamata ya yi ayi maganinsu ta hanya mafi dacewa da bin tafarkin tsarin mulki da ya kasance hanya mafi dacewa mu kare muradinmu dana kasarmu su kasance a sahun farko.

Ka Yi Wa Duk ‘Yan Nijeriya Da Suka Zabe Ka Aiki – Ekiti APC

Tsohon Shugaban jam’iyyar (APC) na Jihar Ekiti Chief Jide Awe,ya bayyana cewa nasarar jam’iyyar a zaben Shugaban kasa na al’ummar Nijeriya ne wadanda suka zabi jam’iyyar lokacin da take fuskantar kalubale.
Awe shi ne mataimaki na musamman na gwaman Ekit kan harkokin siysa, bayyana zaben da jam’iyyar APC ta samu nasarar lashewa ta hanyar dantakarar ta Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wani al’amari ne daga Allah,domin duk wani tunanin da aka yi na siyasa da addini sam sai abin ya kasance ashe ba haka bane.

A hirar da ya yi da mabnema labarai a Ado- Ekiti tsohon Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Ekiti a makon daya gabata,ya jinjinawa masu zabe wadanda suka tsaya kai da fata sai da suka zabi jam’iyyar duk da matsalolin data shiga.Ya ce shi al’amarin samun nasarar Tinubu an dade da tunanin hakan zata iya faruwa.

Ya ce , “Gasu ‘yan jam’iyyar APC, nasarar lashe zaben da aka yi ba tasu su kadai bace abin ga ‘yan Nijeriya ne da suka yanke shawarar zaben APC ba tare da la’akari da matsalolinta ba.

“Tsammanin kowa shi ne Tinubu cikin sauki zai ci Legas a kowane irin zabe,amma abinda ya faru shi da jam’iyyarsa ta sawa ce ta kada su. Hakanan ma ana iya tunanain ‘yan Arewa sune suka tsai da shi amma sai gas hi a wasu nmanyan Jihohin Arewar kamar Sakkwato,Katsina da Kaduna bai samu nasara ba,daga karshe shi yayi nasarar lashe zaben.

Awe ya ce Tinubu bai kasance a matsayin dansiyasa ba kawai shi tamkar mai niyyar lashe wani tsere ne da ya maida hankalinsa ga sai ya samu nasara ko ta yaya ta kasance,rashin gazarwasa da tsoro ya say a samu nasarar lashe zaben duk da yake ya hadu da matsaloli masu yawa.

Shi yasa bayan da aka bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban kasa da aka zaba byan da aka yi zaben Shugaban kasa na 2023, sai ga kungiyoyi sun fara kamun kafa domin samun mukaman siyasa daga wurin gwamnatin tarayya da zata hau kan karagar mulki nan bada dadewa ba.

Binciken da jartidar LEADERSHIP ta yi ya nuna kafin ayi zaben Shugaban kasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu ya kuma samu nasara dan takarar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shi ne dantakarar jam’iyyar,za a rantsar 29 ga watan Mayu ya gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari da zai kammala wa’adinsa na biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here