Daruruwan mayakan Boko Haram sun mika wuya ga sojojin Najeriya

0
104

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce ‘yan ta-da-ƙayar-baya 1,332 ciki har da iyalansu ne suka miƙa wuya ga dakarun Operation Haɗin kai a faɗin yankin arewa maso gabas cikin mako biyu da ya wuce.

Daraktan harkokin yaɗa labaran tsaro Manjo Janar Musa Danmadami ne ya ce ‘yan ta-da-ƙayar-bayan da suka miƙa wuya sun ƙunshi magidanta 222 da mata 411 sai ƙananan yara 699.

Hedikwatar tsaron ta ce tana ci gaba da tantance ɗaruruwan ‘yan ta-da-ƙayar-bayan da suka miƙa a tsawon mako biyun da ya wuce, kafin ɗaukar mataki na gaba a kansu in ji Manjo Janar Musa Danmadami.

Daraktan yaɗa labaran tsaron ya kuma ce dakarun sojin Nijeriya sun kashe waɗanda ya kira ‘yan ta’adda guda 8, sun kuma kama mutanen da ake zargi masu kai musu kayan buƙatun rayuwa ne 35 a daidai lokacin da suka kuɓutar da fararen hula 19.

A yayin taronta na manema labarai duk mako biyu, Hedkwatar Tsaron Najeriya a jiya Alhamis ta kuma ce dakarun ƙasar sun karɓo makamai daga ‘yan ta-da-ƙayar-baya ciki har da bindigogin AK47 guda 14 da harsasan AK47 da bindigar toka 2 da ƙaramar mashinga ɗaya da ɗaruruwan albarusan bindigogin mashinga. Da gurneti 36.

A cewarsa duk kayan da sojoji suka gano da fararen hula da suka kuɓutar da kuma mutanen ta ce sun kama bisa zargin ‘yan ta-da-ƙayar-baya ne, an damƙa su hannun hukumomin da suka dace don ɗaukar mataki na gaba.

Janar Musa Ɗanmadami ya kuma ce an kashe ‘yan ta-da-ƙayar-baya da dama a jerin hare-haren jiragen sama tare da lalata harkokin ta’addancinsu a cikin mako biyun da ya wuce.

Haka su ma dakarun aikin Hadarin Daji a yankin arewa maso yammacin Nijeriya sun samu nasarori da yawa ciki har da kashe ‘yan fashin daji 13 da kuɓutar da fararen hula 23 da aka sace. Sannan sojoji sun ƙwace bindigogin AK47 guda 7 da kurtun harsasan bindigar 12 da albarusai masu yawa

Janar Ɗanmadami ya ƙara da cewa manufar taƙaita kashe takardun kuɗi ta Babban Bankin Nijeriya da ƙoƙarin da sojoji ke ci gaba da yi sun taimaka wajen rage satar mutane don neman kuɗin fansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here