An tsinci gawar mutane 10 bayan harin ’yan bindiga a kudancin Kaduna

0
181

Akalla gawarwaki 10 aka tsinta bayan wani harin ’yan bindiga a kauyen unguwar Wakili da ke Karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.

Tuni dai majalisar Karamar Hukumar ta sanar da sanya dokar hana fita a yankunan Ungwan Juju da Mabuhu da Ungwan Wakili da kuma Zangon Uba.

Karamar Hukumar dai ta sanar da sanya dokar ce a cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Karamar Hukumar, Yabo Chris Ephraim, ya fitar.

Ya ce an sanya ta ne domin dakarun sojoji su sami zarafin dawo da zaman lafiya a yankin.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna ba ta magantu a kan lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here