Dan shekara 13 ya harbe karamar yarinya da bindiga a Ogun

0
125

Wani yaro dan shekara 13 ya harbe wata yarinya ‘yar shekara uku har lahira a kauyen Kukudi da ke Imasayi a karamar hukumar Yewa ta Arewa a Jihar Ogun.

Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Abimbola Oyeyemi, ya bayyana haka a Abeokuta ranar Juma’a, inda ya ce yaron ya harbe ta ne bindigar farauta.

Ya bayyana cewa tuni ‘yansanda suka cafke mai bindigar mai shekaru 45 bisa laifin sakaci.

“Bincike na farko ya nuna cewa ya loda bindigarsa ta farauta kuma ya ajiye ta a wani budadden waje da ke bayan gidansa inda yara kan yi wasa.

“A can ne matashin mai shekaru 13 ya dauki bindigar, ya nuna wa mamaciyar sannan ya dana mata bindigar.

“An kai wacce aka kashe zuwa babban asibitin Ilaro, inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarta,” Oyeyemi ya bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here